<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>A Cikin Duniyan Nan Yanzu LW215</title>
<lyrics>[V1]
 1) A cikin duniyan nan yanzu,
 Ya Ubanjiji, bi da mu.
 Akwai jaraba ko'ina,
 Ka bi da mu da Ruhunka.

[V2]
 KORUS
 Ya Ubangiji, Mai Ceto,
 In ban da kai, ba taimako,
 Ka koya mana nufinka,
 Ka bi da mu da Ruhunka.

[V3]
 2) Ga aiki yana jiranmu,
 Ga tumakinka, ƃatattu,
 Mu je mu kawo su yanzu,
 Ka bi da mu da Ruhunka.
 Korus

[V4]
 3) In za mu shiga yaƙinka,
 Mu yi kokawa da magauta,
 Ka ƙarfafa ƴan yaƙinka
 Ka bi da mu da Ruhunka.
 Korus

[V5]
 4) Idan mun gama aikinka,
 Ka kira mu ga hutawa.
 Ka bi da mu da Ruhunka,
 Ka kai mu Sama lafiya.
 Korus</lyrics>
<hymn_number>215</hymn_number>
<author>Johnson Oatman Jr</author>
</song>